Mai Digiri ta kwafsa” An yiwa Fati Washa ca kan rubuta Turanci ba daidai ba a karon farko bayan kammala karatun ta..

A jiya da daddare ne fitacciyar Jarumar ta wallafa wasu daɗin hotunan ta wanda akayi mata a ranar kammala Degree ɗin ta na farko a kasar Cyprus.

Sai dai rubutun da jarumar tayi wasu na fadin cike yake da kurakurai da rubuta wata kalma ba daidai ba.

Sai dai wasu sun alaƙanta hakan da suɓutar madannan waya,yayin da wasu suke ganin daga gare ta ne.

Haka dai mutane da dama suka cigaba da bayyana ra’ayoyin su a shafukan sada zumunta.

Ga wallafar da jarumar tayi kamar haka,da wani gyara da wata tayi mata a shafin Instagram…