Labari mai daɗi: Jami’an tsaro na KSCWC sun tarwatsa dabar kasurgumin dan bindiga Ɗangote, sun hallaka yaransa 15 a jihar Katsina…

Jami’an tsaron al’umma ƴan-sakai “Katsina Community Watch Corps” na ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun tarwatsa dabar kasurgumin ɗan ta’adda Ɗangote, inda suka hallaka yaransa 15 a wani harin kwantan ɓaure wanda suka farmaki ƴan bindigar.

Katsina Reporters ta samu cewa, Jami’an KSCWC sun ci galabar ƴan bindigar ne, a wani harin kwantan ɓauna da suka kai masu a daji, inda suka fatattakesu tare da hallaka ƴan bindiga 15 da kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47 daga hannunsu.

Ƙaramar hukumar Batsari na daga cikin garuruwan da suke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina inda ake ka-she mutane tare da yin garkuwa da jama’a zuwa daji don neman kuɗin fansa.