Abubuwan da suka haifar wa duniya tsadar rayuwa a halin da ake ciki…

Inda ƙasashen duniya da dama ke cikin wannan matsala, sakamakon tashin farashin abubuwan amfani na yau-da-kullum.

A baya-bayan nan Najeriya da sauran ƙasashen Afirka irinsu Ghana da Nijar na fuskantar matsalar tsadar rayuwa.

To sai dai matsalar ba ta tsaya ga nahiyar Afirka kaɗai ba, al’amari ne da ya shafi duniya baƙi-ɗaya.

Jaridar BBC Hausa na tattaro wannan bayanai Shin me ke haifar da wannan matsala da tsadar rayuwa a faɗin duniya?

1-Tashin farashin makamashi da man fetur

An samu ƙaruwar farashin man fetur tun bayan ɓarkewar annobar korona, inda buƙatar man fetur ɗin ta ƙaruwa a duniya sakamakon matakin kullen korona da ƙashen duniya da dama suka ɗauka.

Wannan abu ya sa man fetur ɗin ya kai tsadar da bai taɓa kai wa ba cikin shekaru masu yawa.

A yanzu dai ana sayar da gangar ɗanyen mai man fetur kan dala 79 zuwa sama a kasuwannin duniya.

Hakan ya faru ne sakamakon yaƙin Ukraine da Rasha, Ita dai Rasha na cikin ƙasashen da suke da arzikin man fertur da iskar gas.

Sakamakon yaƙin Ukraine ya sa ƙasar ta rage adadin man da ke fitarwa zuwa kasuwannin duniyar, sannan kuma takunkuman karya tattalin arziki da wasu ƙasashen duniya suyka sanya mata, ya sa sun dai sayen man ta.

Sannan matakan takunkuman sun sa Rashar ta daina sayar wa wasu ƙasashen Turai man fetur da kuma iskar gas.

Hakan ya sa wasu ƙasashen mayar da hankali zuwa wasu ƙasashen duniya domin sayen man fetur da gas ɗin da suke amfani da shi, hakan ne ya sa farashin man fetur ɗin da na iskar gas ya ƙaru a duniya.

2- Annobar korona