Sojoji sun kuɓutar da mata 18 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina..

A ranar Laraba ne dakarun sojin Najeriya suka yi nasarar kubutar da wasu mata 18 da aka yi garkuwa da su daga tare da mika su ga gwamnatin jihar Katsina.

Kwamandan Birgediya ta 17 ta Rundunar Sojan Najeriya, Katsina, Birgediya-Janar Oluremi Fadairo, ya ce sojojin sun kai wani samame na ceto a maɓoyar yan bindigar da ke dajin Yan-Tumaki da Dan-Ali.

Ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan ta’addan a fafatawa da su ka yi, inda daga bisani suka yi nasarar kubutar da matan.

Daga nan Fadairo ya mika matan ga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Dr Nasiru Mu’azu.

Ya kuma jaddada shirye-shiryen rundunar sojin Najeriya na ci gaba da yin aiki domin maido da zaman lafiya na dindindin a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *