Kyawawan hotunan jaruma Nafisat Abdullahi da bata taɓa yin irin su ba..

A shekaran jiya ne aka gudanar da bikin taya Ali Nuhu murnar mukamin da Tinubu ya bashi na shugaban hukumar finafinai ta kasa.

Jarumai manya,matsakaita da kanana babu wanda bai halarta harma da tsoffin jarumai wadanda aka yi shekaru da dama ba’a ganin su.

Nafisat Abdullahi tana daya daga cikin jaruman da sukayi fice a gurin domin ita ta dauki hankalin kowa a gurin,ma’ana ta dusashe tauraruwar kowanne jarumi dake gurin,an nemi a ga wasu Jaruman da suka halarta amma ina duk ba’a gan su ba domin masu daukar hoto hankalin su yana kan Nafisa.

Ga wasu daga cikin hotunan Jarumar,ku cigaba da kasancewa damu domin samun labarai da ɗumiɗumin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *