An tuhumi wasu mutane hudu bisa laifin satar wani bandaki na zinari da aka kiyasta kudinsa ya kai fam miliyan 4.8, wanda ya bace daga Fadar Blenheim a wani samame na dare da wasu barayi suka kai a watan Satumban 2019, kamar yadda rahoton jaridar Guardian UK ya ruwaito.
A cewar rahoton jaridar, bandakin zinaren, da ake wa lakabi da suna Amurka, wani bangare ne na baje koli na mai zane-zanen Italiya Maurizio Catelan.
A ranar Litinin, hukumar gabatar da kara ta ‘Crown’, ta ce ta bayar da izinin tuhuma kan aikata laifi akan wasu mutane hudu, wadanda za su gurfana a gaban kotun majistare ta Oxford, a ranar 28 ga watan Nuwamba.
Me ake yi da bandakin zinaren?
Bandakin zinaren, wanda za a iya amfani da shi a kayyadadden lokaci na minti uku don kauce wa layi, ya kasance a wajen bajen kolin na tsawon kwanaki biyu kawai, kafin wadanda ake zargin suka sace shi. An ajiye bandakin zinaren ne a matsayin aikin fasaha a fadar Oxfordshire, mahaifar Winston Churchill, lokacin da ya bace.
Kamar yadda aka girke shi a lokacin, cire shi ya haifar da ambaliya da lalacewar kyakkyawan gidan da ya wanzu tsawon karni 18 da kuma wani sashe na wurin tarihi na Unesco a Woodstock.
Gidajen tarihi da aka taba ajiye bandakin zinaren
A cewar rahoton jaridar The Punch, an taba sanya bandakin zinaren a gidan kayan tarihi na Guggenheim da ke New York, a shekarar 2016, inda mutane 100,000 suka yi layi don amfani da shi. Daga bisani aka yi kaura da shi zuwa Blenheim, inda aka ajiye shi a cikin dakin da ke fuskantar dakin da aka haifi Churchill, a wani wasan kwaikwayo na farko da Cattelan ta Birtaniya za ta gabatar bayan fiye da shekaru 20.
