https://nounrespectively.com/99/54/39/995439caf4e551e612393deb186603a4.js'

 SHARI’AR ZABEN KANO: A Yau Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano..

A Yau Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano

Kotun ɗaukaka ƙara za ta fara sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar kano…

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a Abuja za ta fara sauraron ƙarar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP suka shigar gabanta, don ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar.

Daukaka ƙarar dai ya biyo bayan hukucin da kotun sauraran ƙararaki zaɓen gwamann jihar ta yi a ranar 23 ga watan Satumbar da ya gabata, inda ta bayyana Dr Nasir Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya yi nasara a zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar sa ta NNPP ne dai suka ɗaukaka ƙara bayan da kotun saurarar ƙararrakin zaben gwamnan jihar ta soke ƙuri’u 165,663 daga jimillar waɗanda suka samu a zaɓen da ya gabata.

Kotun ta ce ta soke kuri’un ne sakamakon rashin sanya hannu da stamfi a kan ƙuri’un da hukumar zaɓen ƙasar ta INEC ba ta yi ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *