https://nounrespectively.com/99/54/39/995439caf4e551e612393deb186603a4.js'

Rundunar sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe gomman gawurtattun ‘yan ta’adda a wani hari na musamman da suka kaddamar a jihar Sokoto da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Talata.

Ya ce dakarun sojin Nijeriya sun kaddamar da “samame da aka tsara cikin nutsuwa a kauyen Tukandu don murkushe wata kungiyar gawurtattun ‘yan ta’adda da ke da alhakin aikata laifuka da dama a yankin.”

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarunsu sun kaddamar da “samame da aka tsara cikin nutsuwa a kauyen Tukandu don murkushe wata kungiyar gawurtattun ‘yan ta’adda da ke da alhakin aikata laifuka da dama a yankin.”

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *