https://nounrespectively.com/99/54/39/995439caf4e551e612393deb186603a4.js'

Zuwa gareku MAZA DA SABIN ANGW/AYE

Wani ne ya turomin sago akan zaiyi aure yana neman shawara da “dos and dont” na aure.

Naga ya dace in yi posting may be akwai wadda zasu amfana, duk da nasan abune mai wuya cikin dan gangani lokaci da rubutu a fadi abunda ke cikin aure tunda wani abun sai ka shiga zaka gani ko ka gane.

So below is what I send him :-

Ka sani aure ibadane a cikin dukkan ibada da ruyawar akwai jarrabawa a cikin sa, hakuri, kiyaye dokokin da Allah da koyi da sunnan Annabi zai kaika ga cin nasara a ciki.

Ka sani Amanace a wajen ka kuma Allah zai tambayeka akan amanar da aka damqama.

lyayenta sun baka ita ne dan kyauta zato a gareka akan ‘yar su zata samu kuluwa da farin ciki a wajen ka, sabida haka kazama gatanta, karka sake ka samarmata da aqasin haka domin zai nuna gazawarka da qasqanci a matsayin ka na jagora.

Kiyaye dukkan hakkokinta da ya rataya akan ka.

Ka sani ita mace da kyauta da kyautata mu’amala aka fi sace zuciyarta, ka kasance mai kyautatawa a cikin kalamanka wajen mata gyara da kiyaye furta abunda zai cutar da zuciyarta, ka kyautata a cikin ciyarwa, tufatarwa, muamalantarta da ‘yan uwanta.

Ka sani mace halittace mai taushi zuciya da raunin hankali, wani lokaci zakaga abunda kake so wani lokaci sai kayi hakuri matugar hakuri da kawaici da ita.

Ka sani kai jagora a gidanka dan haka dole kakasance abun koyi a cikin dabi’u da halaye a cikin gidanka. Kar ka bari munanan dabiun ka ya zama abun kyama da zargi a cikin gidan ka, matuqar baka kiyaye naka ba zaiyi matuqar wuya ta iya kiyaye nata, wadda yin hakan zai zama silar fititintunu a auren ku.Kiyaye tsabtar jikinka, babu wadda yake son kusantar kazamin mutum, ka kasance mai kiyaye tsabtar jikinka a duk lokacin da zaka kusanci matarka, wannan zai samar mata da nitsuwa a zuciyarta da zata mu’amalance ka cikin kwaniyar aurenku cikin sauqi.Bayan tsabta, askin sama da qasa da yin brush atleast safe da dare, Ka riqe turare dan shine zai zama dan sagonka zuwaga matarka cikin sauqiKa kiyaye shigan ‘yan uwanka al’amuran rayuwar gidan ka ko tsakaninka da matarka, cikin saugi in baka iya tsayarda kowa a matsayar sa ba zaa dagulama lissafi da rayuwar gidanka akan abunda bai kai ya kawo ba a hanaka zaman lafiya da jin dadi da iyalanka.A duk lokacin da kuka samu matsala ka bada kofar zama tattaunawa a tsakanin ku domin shine kofa mafi saugin samu gyara, mafita da maslaha a tsakanin maaurata.Matarkace, ka karanceta kasan waye ita da yadda take muamalantar mutane, Karka bari wani ko was su zo suna fadama waye matarka domin aqasarin lokaci qarya ko sharrinta za’a fadama ba

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *