https://nounrespectively.com/99/54/39/995439caf4e551e612393deb186603a4.js'

An samu wani hazikin yaro mai shekera 12 da ya haddace Alqura’ani mai girma a Katsina …

Wani dan makarantar Firaimare mai suna Mahmud Mahmud daga garin Gangara na karamar hukumar Malumfashi ya haddace Alqura’ani mai girma yana da shekaru sha biyu (12) kacal a duniya.

Sakataren ilimi na karamar hukumar ta Malumfashi, Alhaji Musa Ibrahim Wanzamai ne ya jagoranci yaron tare da wasu. 

sauran yaran daga karamar hukumar zuwa garin Daura inda aka gudanar da wata jarabawar zakulo yara yan baiwa da za a ba gurbin karatu a makarantar yan baiwa dake garin Minna jihar Neja.

Makarantar dake Minna ta yi suna sosai wajen zakulo yara masu basira daga dukkan sassan kasar nan tare kuma da basu kyakkawan ilimi domin samar da cigaba mai dorewa ga ɗaukacin al’ummar Najeriya da ma duniya baki daya. 

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *