https://nounrespectively.com/99/54/39/995439caf4e551e612393deb186603a4.js'

Fiddausi yar Tiktok tayi wani faifan bidiyo ne inda take ikirarin zatayi jigidar bama-bamai inda take lissafo mutane da zata iya kunar bakin wake tun daga kan alkaliyar yar zuwa ga mai girma mataimakin shugaban kasar Kashim shettima da shugaban jam’iyyar Apc na kasa Dr. Abdullahi umar Ganduje da dan takarar gwamna jihar kano Dr.nasiru Yusuf gawuna wanda kotun sauraren kara ta tabbatar a matsayin wanda ya lashe zaben kano.

Ni gaskiya kawai na fada ne amma banida alaka da bom rai nane ya ɓace dukan abunda na fada ina rokon tun daga mai girma mataimakin shugaban kasa da Dr. Abdullahi umar Ganduje da Dr. Nasiru Yusuf gawuna da dai duk wanda na taɓa a bidiyon Dan Allah yayi hakuri ya yafemin in sha allahu bazan kara ba.

Sa’a nan hukuma ma ina rokonta da tayi hakuri ta yafemin insha Allah wannan zai zamanto izina a gare ni.- inji Firdausi Yar Tiktok.

Itama mahaifiyar ta da yar uwarta da suka je karba ta sun bayyana godiya baza’a kara jin tace zata daura bam ba.

In sha Allahu zan sa ido sosai in gani bazata kara yi ba kuma na gode da jami’an tsaro Allah ya saka da musu da Alkhairi -inji mahaifiyarta.

“In sha Allahu bazata kara ba zamu tsaya sosai tsayin daka a kanta in Allah ya yarda wannan ya zamo izina a gareta Allah kuma ya karemu baki daya.”-inji yar uwarta

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *