SAI DA NA ZUBAR DA HAWAYE DA NA KARANTA LABARIN NAN 😠Kalli Cikakken Bidiyon…..
~ Muna zaune muna tattaunawa da safe kamar karfe 9 na safiyar ranar Laraba 20 ga watan September 2023 da kanwar Mahaifina, muna magana har dai hirar ta kaimu ga zancen wani mutum Bawan Allah, sai take sanar dani cewa an zalunce shi, an cutar dashi, an ‘daure shi a Gidan Yari na tsawon shekaru 4 zai shiga shekara ta biyar a yanzu haka.
~ Nan da nan na tashi naje Gidan Yarin, na nemi izini ina son ganin sa, aka yi mun duk binciken da za’a yi, na cike duk wata ka’idar ganin mutum a Gidan Yarin, na shiga na ganshi, yana fitowa sai na ganshi da Haiba, Kamala, da Cikar fuska, yana sanye da Gilashi a Idon sa, Saurayi cikakke abun burgewa.
Sai na tattauna dashi, tattaunawar gata kamar haka:
Nace ‘dan uwa ya kake, yace lafiya lau Malam, Alhamdulillah, nace muna zaune da Hajiya (…..) muna tattaunawa sai muka biyo kan labarin ka, sai take ban labarin ka, wallahi ban san ka ba, ban san labarin ka ba sai yau (Laraba 20 September 2023).
~ Yace Allah Sarki, sannu da zuwa, nace yauwa. Nace ‘dan uwa shekarun ka nawa? sai ya fada mun sai naga ai kusan shekaruna da nasa ‘daya ne. Nace shekarun ka nawa a Gidan Yarin nan, yace hudu tun 2019.
Nace me ya faru har kazo nan? yace sharri aka yi mun, wata mata ce tayi mun sharri, cewa wai na nemi nayi lalata da ita, alhali karya ne. Mijin ta babban mutum ne yana Kudi, sai kawai aka kama ni aka daure ni, ina zaune a nan shekaru hudu. Nace a lokacin da aka kama ka kana karatu ne? Yace eh ina karanta Law har na kai 400 level a University.
~ Nace a ina ka hadu da matar har tayi maka wannan Qazafi? yace ina koyar da ‘ya’yan su Al-Qur’ani da Hadisai ne a gidan su ana biya na duk wata, sai tayi mun wannan Qazafi.
Nace anyi bincike akai, yace Eh anyi, an tabbatar bani da laifi, anje gaban hukuma, anje Kotu, shine suka ce a daure ni, ni kuma na karbi Qaddarar. Daga baya tazo tace wa Mijin ta wallahi wallahi karya tayi, sharri tayi mun, ta kira Mama na a waya tace kiyi hakuri sharri nayi wa ‘danki.
~ Nace yaushe tayi haka? yace bayan shekara daya da shigowa ta Gidan Yari, yanzu shekaru uku da gano gaskiyar Amma ana rike da Kai? yace Eh.
Jama’a babban abinda zai baku mamaki sune wasu abubuwa guda 6 dana Ciro su daga tattaunawar mu:
1. Na farko Mahaddacin Al-Qur’ani ne.
2. Na biyu, wannan Sallar Layyar data wuce Mahaifiyar sa tayi masa dinkin sallah kala Goma zata kawo masa Gidan Yarin sai Mota ta buge Mahaifiyar sa, nan take ta rasu.
3. Matar da tayi masa sharrin Zina yanzu haka ta makance bata gani da Idon ta.
4. Mijin ta yayi Hatsari, an yanke masa ‘kafa yanzu haka.
Matar da tayi masa sharrin tana da ‘Ya’ya uku, sunyi tafiya (su Yaran) suka yi hatsari a Mota, wata Trailer ta markade su gaba daya suka mutu, su Yaran.
Bala’i da fitin-tinu kullum Hawa kan matar suke yi, tana kasuwanci yanzu kasuwar ta rushe bata da komai.
(matar tayi ta aikewa da sako cewa don girman Allah ya daina yi musu addu’a haka, sun ga bala’i iri iri a shekaru hudun nan, yayi hakuri ya yafe mata).
6. Yace mun, saboda an tabbatar baya da laifi har an bashi dama yayi Degree daga Gidan Yarin, ya kammala yanzu haka yana masters dinsa. Yana business dama, ya samu wasu matasa masu gaskiya da Amana sun rike masa Kasuwancin sa da gaskiya.
Nace me yasa matar ba zata zo ta saka hannu ta tabbatar sharri tayi maka ba, yace suna tsoro ne, bayan sun wahalar dani yanzu idan suka dawo suka ce karya suka yi ita matar za’a kama a daure. Kuma matar babban mutum ne, Asirin su zai tonu, zasu ji kunya.
~ Yace abinda aka yi guda ‘daya ne, shine an rubuta sunana daga cikin wadanda Gwamna zai yafe musu, irin Afuwan nan da Gwamnati take yiwa ‘yan Gidan Yari duk shekara, toh an Saka sunana, muna zaton a cikin watan October mai zuwa 2023 din Nan za’a fitar dani.
~ Nace me kake so yanzu nayi maka na taimako?
Yace Ina so ka taya ni addu’a. Nace bayan wannan fa? Nima field dinka na karanta Law nayi, yace ma sha Allah, yanzu mun tsallake wajen da ake bukatan Lauyoyi, Gwamnati ne kawai muke jira ta yafe mana.
~ Wani abun mamaki kuma👇
~ Nace masa an bani Lambar wayar budurwar ka tun kafin nazo nan, nayi waya da ita, itace ma tayi ta taimaka mun har na shigo nan, yace Allah Sarki. Yarinya ce karama, ta tsaya sai shi din, tayi hakuri tsawon shekarun nan, iyayen ta sun karfafe ta akan sa, cewa tayi hakuri, tace babu komai, idan ya fito za suyi aure.
~ Yace yanzu kaga a gidan Yarin nan na Haddatar da mutane da yawa Al-Qur’ani, da yawa sun san Musulunci sun shiryu. Yace mun yana Azumin Litinin da Al-Hamis duk Sati, kuma yana tsayuwan dare, yace babu wata mummunar addu’a da yake yi ma wancan matar, jarabawar Allah ne kawai yake hawa kanta.
Yace Barrister menene sunan ka, ina so mu saba ka zama ‘dan uwana, nace sunana Abdul-Hadee, yace ni kuma sunana (……) Nace ma sha Allah.
~ Nace masa daga labarin ka na fahimci kana kusa da Ubangiji, ina maka kyakkyawan zato kana da wani matsayi a wajen Allah abun girmamawa Ina so kayi mun addu’a, yace Babu komai zan maka, da Kai da kanin ka Ibraheem Isah Ibraheem da kuka shigo.
Nace nagode sosai, zan tafi Abuja this week, idan na dawo zan sake dawowa, na karbi lambobin wayar wasu Ma’aikatan wajen domin idan zan je na dinga contacting dinsu.
Yace Malam Abdul nagode, nagode, kamar zai yi hawayeðŸ˜, nace karka damu ‘dan uwa.