Wasu hotunan kafin Aure na wasu Hausawa dai suna cigaba da tayar da kura a shafukan sada zumuntar zamani da suka hada da Fezbuk, Tuwita da kuma Instagram a ‘yan kwanakin nan.
Hotunan dai na wasu ne da ake kyautata zaton aure za suyi a ‘yan kwanakin nan masu zuwa da kuma suka je suka dauki hotunan na kafin aure, kamar dai yadda zamani ya kawo.
Hausa ta samu cewa hotunan na dauke ne da namijin wanda yake kama da ya taba yin aure kuma ya girmi matar sosai yayin da ita kuma ake tsammanin bata taba aure ba kamar dai yadda hotunan suka nuna.
Sai dai al’umma da dama da suka ga hotunan sun bayyana cewa matar kudi ne kawai ta gani amma ba wai tsantsar soyayya a tsakanin su inda suke ganin ba yadda za’ayi ace tsoyayyar tsakani da Allah ce.
Wasu kuma na ganin cewa shi daman so ai Allah ne ke dasa shi a cikin zukata kuma ba tare da shawara ba kuma suna ganin su wannan gamon jini ne kawai.
A hotunan dai an ga matar cike da annashuwa inda a wasu wuraren ma ta kwanta a jikin sa cike da shauki na kauna.